in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun Amurka sun musunta jita-jita game da koman bayan tattalin arzikin Sin
2016-03-10 10:37:57 cri
Game da shaci-fadi da wasu mutanen suka yi wa tattalin arzikin Sin, kwanan baya, kwararrun kasar Amurka sun bayyana cewa, an canja salon raya tattalin arzikin Sin lami lafiya, kuma sha'anin ba da hidimomi ya kasance jigon raya tattalin arzikin Sin, wanda zai magance koma bayan tattalin arzikin kasar cikin dan kankanin lokaci.

Manazarci a cibiyar nazarin tattalin arzikin kasa da kasa Peter G. Peterson ta kasar Amurka NicholasR.Lardy ya rubuta wani bayani, inda ya bayyana cewa, shaci fadin da aka yi a kan tattalin arzikin Sin ya mayar da hankali ne game da tafiyar hawainiya da yadda ake raya masana'antun Sin, amma bai lura da sha'anin ba da hidimomi da ya kai rabin GDP wajen ingiza karuwar tattalin arzikin Sin ba.

Lardy ya ce, yanzu, akwai fannoni 5 da suka suka taimaka ga samun karuwar tattalin arzikin Sin, wadanda suka hada da karuwar kudin shiga wanda zai kara harkar sayayya, kuma Sin ta kasance daya daga cikin manyan kasashen da suke samun kudin shiga mafiya yawa a duniya, idan kasar ta ci gaba da samun bunkasuwa, hakan zai kara ingiza yawan sayayyan da ake yi a kasar. A cikin shekaru 10 da suka gabata, an bullo da tsarin ba da kudin inshora ga zamantakewar al'umma yadda ya kamata, kuma an samu raguwar masu ajiye kudi a bankuna, dadin dadawa kuma, bayan da aka yi garambawul game da tsarin musayar kudi, matakin ya jawo hankalin masu zuba jari a sha'anin ba da hidimomi a maimakon masana'antu. A karshe kuma, sha'anin ba da hidimomi yana bukatar ma'aikata da yawa, hakan zai taimaka iyalai kara samun kudin shiga.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China