A tsawon kwanaki biyar, mahalarta taron za su saurari da tattauna kan rahoton darektan game da ayyukan WHO a nahiyar Afrika tsakanin shekarar 2014 zuwa shekarar 2015, da kuma sauran batutuwan da suka jibanci kiwon lafiya, in ji Dokta Matshidisco Moeti, darektan WHO reshen Afrika.
Daga cikin batutuwan da za a tabo, akwai cigaban da aka samu kan ayyukan cimma burin muradun sabon karni na bunkasuwa dake nasaba da kiwon lafiya da tsarin cigaban kiwon lafiya na bayan shekarar 2015, da ma dabarun duniya kan gudanar da ayyukan kula da lafiyar jama'a, bincike kan kiwon lafiya da kokarin jama'a domin kiwon lafiya.
Mista Matshidisco Moeti ya kara da cewa, kwamitin shiyyar zai kuma tattauna game da asusun Afrika kan ayyukan gaggawa na kiwon lafiya ga jama'a, annobar cutar Ebola ta shekarar 2014, matsalar cutar shan inna da kuma tsare tsaren shiyyoyi wajen aiwatar da kasafin kudin tsarin WHO na shekarar 2016 zuwa shekarar 2017. (Maman Ada)