Kasahen Rwanda da Burundi da kuma jamhuriyar demokaradiyyar Congo ne zasu amfana da aikin.
Za'a kasafta wutar lantarkin ne tsakanin kasashen 3, inda kasar Rwanda zata amfana da megawatts 50 na lantarkin.
Ministan kudin kasar Rwanda Claver Gatete shine ya rattaba hannu kan yarjejeniyar rancen kudaden aiki a madadin kasashen ukun, sai kuma jami'in bankin AfDB dake Rwanda Negatu Makonnen.
Gatete ya ce, aikin zai taimaka wajen samar da ingantaciyyar wutar lantarki a shiyyar.
Negatu Makonnen wakilin na AfDB, ya fada cewar, samar da ingantattun ababen more rayuwa, zai taimaka wajen dunkulewar shiyyar musamman ta fuskar manyan kalubalan da ake fuskanta na sauyin yanayi da kuma tsaro. Ahmad