Dorewar ci gaban kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara ba zai yiwu ba, sai bangaren makamashi na kunnen doki tare da ayyukan ci gaban kasashe, in ji wani rahoton kungiyar kasa da kasa ta kamfanonin da suka kwarewa kan ayyukan bincike, ba da shwarwari da harkokin haraji, KPMG da aka fitar a ranar Talata a birinin Cape Town a jajibirin dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2015 kan nahiyar Afrika da aka tsai da shiryawa a ranakun 3 da 5 ga watan Yuni.
A cewar wasu hasashe, dalar Amurka biliyan 300 ake bukata domin baiwa kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara damar samun wutar lantarki a tsawon shekaru goma sha biyar masu zuwa.
A halin yanzu, shiyyar na iyar samun wutar lantarki kashi 25 bisa 100 kawai, wato kimanin kashi 1 bisa 6 na matsakaicin matsayin duniya, idan aka yi la'akari da shan wutar lankarki na ko wane iyali. (Maman Ada)