Bankin raya Afirka na AFDB ya bayyana cewa yanzu haka yawancin kasashen Afirka na fuskantar matsalar katsewar wutar lantarki, matakin da ke jefa al'ummar nahiyar su kimanin miliyan 620 cikin matsalar karancin wutar.
A kwanakin baya ne dai Jaridar "This Day" dake Najeriya ta rawaito bankin na AFDB na cewa yawan hasarar da wannan matsala ke haifarwa ga tattalin arzikin kasashen na Afirka, ya kai dalar Amurka biliyan 30 zuwa 40 a ko wace shekara. Adadin da ya kai kashi 1 zuwa 2 cikin dari bisa jimillar GDPn daukacin nahiyar.
Haka zakila, kusan rabin muhimman ayyukan more rayuwa da Afirka ke bukata, na da nasaba da samuwar wutar ta lantarki. Domin kaiwa ga samar da wutar lantarki yadda ya kamata gwargwadon bukatar jama'a, bankin ya zuba jarin kudi har dala biliyan 1.9 a shekarar 2014, domin raya wasu ayyuka a wannan fanni. (Kande Gao)