in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan na shirin bunkasa samar da lantarki nan da shekarar 2020
2015-08-03 10:00:08 cri
Mahukunta a kasar Sudan na shirin zartas da wani kuduri na bunkasa samar da wutar lantarki tsakanin shekarun 2015 zuwa 2020.

Kwamitin kwararru na bunkasa tattalin arziki, karkashin majalissar ministocin kasar ne ya amince da kundin dake kunshe da wannan kuduri, wanda ya tanaji samar da karin lantarki har mega wat 3,155 ta amfani da karfin ruwa da kuma zafi, matakin da ake fatan zai cike gibin lantarkin da kasar ke bukata.

Wata sanarwa da majalissar ministocin kasar ta fitar a jiya Lahadi, ta ce an gabatar da kundin ne ga ma'aikatar albarkatun ruwa da lantarki, ya kuma tanaji daga matsayin yawan lantarkin da kasar ke samarwa ta karfin ruwa daga mega wat 1,500 zuwa 2,000 kan awa daya.

Ana sa rana lantarkin da ake samarwa daga zafi a kasar ta Sudan zai karu daga mega wat 900 zuwa 3,555 nan da shekarar ta 2020. Za kuma a hada turakun lantarkin kasar da garuruwan Darfur, da Blue Nile da kuma yankin kudancin Kordofan, wanda a yanzu ke fama da tashe-tashen hankula tsakanin dakarun gwamnati da na mayakan 'yan a ware.

Yanzu haka dai wasu sassan kasar Sudan na fuskantar karancin lantarki, wanda hakan ke haifar da damuwa daga bangaren al'ummu mazauna biranen kasar, ciki hadda mazauna birnin Khartoum fadar mulkin kasar.

A watan Disambar bara hukumar UNDP ta MDD ta yi gargadin cewa Sudan na iya fuskantar matsalar lantarki a nan gaba, muddin mahukuntan ta basu dauki wasu matakai na magance kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China