Kamfanin ayyukan lantarki na kasar Sin Sinotec, ya kammala wasu manyan ayyukan lantarki a yankin Gwagwalada dake birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, aikin da zai fadada samar da wutar lantarkin a sassan birnin.
A ranar Litinin ne dai mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo, ya jagoranci bude ayyukan da kamfanin ya kammala cikin watanni 14, ciki hadda kafa wasu na'urorin sarrafa wutar lantarki, da kuma turakun lantarki masu yawa.
Yayin da yake tsokaci game da aikin a wajen bikin mika shi ga gwamnatin Najeriyar, mataimakin babban daraktan kamfanin na Sinotec Bu Songbo, ya ce, aikin shi ne irin sa na farko mafi girma a dukkanin yankin yammacin Afirka.
A nasa bangare, ministan harkokin makamashi a Najeriya Chinedu Nebo, cewa ya yi, aikin, wanda aka gudanar karkashin babban tsarin bunkasa samar da lantarki na kasar, na da matukar muhimmanci ga manufar da aka sanya gaba.
Nebo ya ce, kamfanin lantarki na kasar ne ya baiwa Sinotec wannan aiki, wanda shi ne bangare na biyu a kwangiyar da sassan suka aiwatar, aikin da kuma ke ba da karfi ga samar da lantarki ta amfani da ruwa a yankunan arewacin kasar. (Saminu)