in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin Uganda ta musanta rahoton kama hafsan sojin a kan zaben shugaban kasar
2016-02-20 12:12:29 cri

Sojin kasar Uganda ta musanta rahotannin dake cewa wai an kame Hafsan sojin ta Janar Katumba Wamala, gabanin sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi ranar 18 ga wata.

A sanarwar da ta yi a ranar Jumma'a, kakakin sojin laftanar kanar Paddy Ankunda ya shaida ma kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua cewa, wannan labarin a kan shafukan sada zumunta na da nufin kawo rudani ne kawai da tada rikicin zabe.

Kanar Ankunda, ya ce jita-jitar na da nufin bada wani yanayi cewar ko a cikin rundunar tsaron ma akwai rashin jituwa gabanin sanar da sakamakon zaben.

Ya nuna takaicin shi a kan yadda mutane ke shirya irin wannan zargi ba tare da la'akari da tsaron kasa ba. Yana mai bayanin cewa, rahoton a kan shafukan sada zumunta ya nuna cewar, Janar Katumba ya ki bin umurnin aika sojoji wassu sassan Kampala babban birnin kasar dake yawan samun tashin hankali.

Tun da farko ranar Jumma'a, tashin hankali ya barke a wassu sassan Kampalan lokacin da aka shiga kwanaki biyu na kirga kuri'un.

Dan takarar shugaban kasar na jami'iyar adawa Kizza Besigye, 'yan sanda sun dan rike shi na wani lokaci a wajen taron jam'iyyar shi ta Forum for Democratic Change. Wannan rike shi da aka yi da kuma sakin nashi ya dan kawo hargitsi.

'Yan sanda sun yi amfani da borkonon tsohuwa don watsa taron jama'a a cibiyar jam'iyyar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China