A cikin sakon da ya aike domin ranar duniya na tunawa da wadanda suka fuskanci zamanin da kuma kasancewa cikin wadanda aka yi cinikin su a matsayin bayi, Mr Ban ya ce al'adu da gargajiya na musamman na 'yan Afrika zai cigaba da kyautata rayuwan kasashen da a baya suka kasasance cibiyoyin cinikin bayi.
A kowane shekara tun daga shekara ta 2007, MDD ta kebe ranar 25 ga watan Maris musamman domin tunawa da fiye da mutane , maza da mata da yara miliyan 15 da suka sha wahala suka kuma hallaka a lokacin fiye da shekaru 400 da aka yi na cinikin bayi, mafi girman hijiran mutane da aka taba samu a tarihi.
Ranar duniyar da aka kebe yana da zummar kara fadakar da al'umma ne game da hadarin da ke tattare da wariyar launin fata da kuma abin da zai haifar a yau.
Taken ranar a wannan shekarar shi ne " Tuna da bautan bayi : bikin abubuwan gado da al'adu na Afrika dake waje da kuma asalin su".(Fatimah Jibril)