Dandalin jin kai na duniya ya kasance wata dama guda domin ingiza aikin kawo sauyi da kuma aike da sako na hadin kai da tallafawa mutane fiye da miliyan 125 da ke cikin mawuyacin hali mai tsanani, in ji mista a yayin wannan taro na shiryawa a cibiyar MDD da ke birnin New York na Amurka.
Mista Ban ya jinjinawa kokarin da kasashe da dama suka yi na shirya shawarwari na shiyoyi, da kasidu da sauran batutuwa daga dukkan fannoni. Haka kuma ya bayyana godiya ga kasashe da dama mambobi da suka shirya shawarwari na cikin gida ko taimakawa dandalin jin kai na duniya bisa taimakon kudi da kayayyaki. (Maman Ada)