Ziyarar wacce suka fara daga ranar Litinin data gabata za'a, kammala zuwa ranar 14 ga wannan wata, kuma ta shafi filayen wasa 6 dake biranen kasar da suka hada da St. Petersburg, da Nizhny Novgorod, da Volgograd, da Samara, da Yekaterinburg da kuma filin wasa na Sochi.
A filin wasa na Sochi za'a binciki yadda tsarin sa yake, da irin kayayyakin da za'a tanada don sake kawata shi. Bugu da kari, za'a gudanar da tattaunawa game da duba yiwuwar samar da Karin filayen wasan wadan da a yanzu haka ba'a gina su ba, a biranen Kazan, da Kaliningrad, da Moscow, da Rostov-on-Don, da kuma Saransk.
Tawagar wakilai masu ziyarar sun hada da babban daraktan kwamitn tsare tsaren shirya gasar wasannin na "Russia-2018" Alexei Sorokin, da darakta sashen wasanni na FIFA Colin Smith, da kuma shugaban sashen shirya wasannin kwallon kafa ta duniya na FIFA Chris Unger.
Tawagar dai ta kunshi kwararru a fannonin kawata filin wasa, da shirye shirye da aiwatar da gasa, da tsaro, da sufuri, da bangaren gudanar da zirga zirga, da harkokin kiwon lafiya, watsa shirye shirye ta talabijin, manhajar shafukan yanar gizo, da kula da ma'akata, da kasuwanci, da kuma shirya tikiti.
Haka zalika tagawar ta hada da wakilai daga ma'aikatu da hukumomi dabam dabam na kasar Rasha.(Ahmad Fagam)