in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Infantino ya lashe zaben shugabancin FIFA
2016-03-01 14:48:32 cri
Wakilan hukumar wasan kwallon ta duniya FIFA, sun zabi Gianni Infantino a matsayin wanda zai maye gurbin Sepp Blatter a matsayin sabon shugaban hukumar.

Blatter dai shi ne shugaban hukumar ta FIFA tun daga shekara ta 1998 ya zuwa 2015. A ranar Juma'a ne wakilan FIFAr su 207 suka jefa kuri'un su, a zaben da aka kada a birnin Zurich, bayan da dan takara Tokyo Sexwale daga Afirka ta kudu ya janye daga takarar.

Dole ne dai dan takara ya samu kaso biyu bisa uku na daukacin kuri'un kafin ya samu nasara a zaben shugabancin hukumar ta FIFA. Sai dai bayan kada kuri'un na wannan karo, Infantino ya samu kuri'u 88 ne, sai kuma Shugaban hukumar AFC Sheikh Salman mai kuri'u 85, yayin da yariman Jordan Ali bin al-Hussein ya samu kuri'u 27, sai kuma Jereme Champagne mai kuri'u 7.

Kuma kasancewar ba a samu dan takara guda da ya samu yawan kason da ake fata ba, yasa aka gudanar da zagaye na biyu wanda ya tanaji lashe zaben ga duk wanda ya samu kuri'u mafiya yawa. A kuma wannan karon ne Infantino ya lashe kuri'u 115, yayin da shi kuma Salman ya samu kuri' 88.

A jawabin sa na amincewa da sakamakon, Infantino ya ce yana fatan dawo da martabar hukumar FIFA, ta yadda daukacin al'ummar duniya za su yi alfahari da ita. Kaza lika zai yi aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen sake ginin hukumar, ta yadda hakan zai karawa sha'anin kwallon kafa daukaka. Ya ce hukumar FIFA ta sha fama da manyan matsaloli, amma a yanzu lokacin hakan ya wuce. A cewar sa yanzu lokaci ne na aiwatar da sauye sauye cikin adalci ba kuma tare da rufa rufa ba.

Infantino dai zai jagoranci FIFA har ya zuwa shekarar 2019, lokacin da za a sake zaben shugaban hukumar na gaba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China