Shugaban kwamitin ladaftarwar FIFA Cornel Borbely, shi ne ya bada shawarar zartas da wannan hukunci kan Valcke, bayan kammala binciken da aka yi a kan sa game da karya dokar aiki, da tona asirin hukumar. Borbely, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yana mai cewa za a iya kuma tsawaita dakatarwar da aka yi masa daga kwanaki 90 zuwa wasu kwanakin 45.
A cikin watan Oktoba ne aka dakatar da jami'in har tsahon kwanaki 90, wata guda bayan da aka bukace shi da ya dakatar da shiga harkokin hukumar ta FIFA. Kafin sabon matakin da ake nufin dauka kan Valcke, zai kammala wa'adin dakatarwar dake kan sa ne a ranar Talatar da ta gabata.
Alkalin kotun da'ar ma'aikata Hans-Joachim Eckert, wanda ya tabbatar da hukuncin da aka yankewa Sepp Blatter da Michel Platini ne ake sa ran zai tabbatar da hukuncin da aka yankewa Valcke ko kuma akasin hakan.(Saminu Alhassan)