160324-babban-kamfanin-sin-dake-tallafawa-fifa-na-sa-ran-samun-karin-karfin-fada-a-ji-wajen-shirya-gasar-cin-kofin-duniya-bello.m4a
|
Shugaban na Wanda, Wang Jianlin, ya fadawa manema labaru a Litinin din data gabata cewar, muddin kasar Sin ta bukaci karbar bakuncin gasar cin kofin duniya, babu tantama Mista Wang zai amince da bukatar hakan.
Wang ya fadi cewa, a halin yanzu wasu kamfanonin kasar Sin 2 suna tattaunawa da FIFA game da batun tallafawa hukumar da dimbin kudi.
Ya kara da cewar, akwai alamun wasu Karin kamfanonin na kasar Sin zasu shiga cikin wannan aniya. Kuma ya tabbatar da cewar yana da kwarin gwiwa na yiwuwar Sin za ta iya samun nassrar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya, muddin dai gwamnatin kasar ta ayyana bukatar yin hakan.
A makon jiya ne Wang, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta hulda da hukumar FIFA, a gasannin cin kofin duniya daban daban har zuwa shekarar 2030.(Ahmad Fagam)