in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan hukumar kwallon kafar Kenya na da burin zabar Salman a matsayin shugaban FIFA
2016-02-17 09:18:03 cri

Wakilan hukumar kwallon kafar kasar Kenya, sun ayyana aniyar su ta zabar Salman Sheikh daga kasar Bahrain, a matsayin sabon shugaban hukumar FIFA, yayin zaben hukumar dake tafe cikin mako mai zuwa.

A cewar shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Kenya Nick Mwendwa, matakin na su na da nasaba ne da kudurin da hukumar kwallon kafar Afirka wato CAF ta dauka na goyawa Salman baya.

A makon da ya gabata ne dai hukumar ta CAF ta yanke shawarar goyon bayan Salman dan asalin kasar Bahrain, a wani zama da ya gudana a birnin Kigali. Hakan dai na zuwa ne mako guda bayan da aka zabi Mwendwa a matsayin sabon shugaban hukumar kwallon kafar ta Kenya.

Mr. Mwendwa ya ce zabin Salman ya dace da kudurin hukumar CAF na marawa wanda zai tallafawa Afirka ta fuskar kwallon kafa baya.

Yanzu haka dai 'yan takara 5 dake neman mukamin FIFA sun hada da sakataren UEFA Gianni Infantino, da shugaban hukumar kwallon kafar kasar Jordan yarima Ali, da Sexwale na Afirka ta kudu, sai kuma tsohon mai baiwa hukumar FIFA shawara wato Jerom Champagne, da kuma yarima Salman.

Salman, da Infantino, da Sexwale da Champagne dukkanin su sun ziyarci taron wakilan CAF a kasar Rwanda domin neman goyon bayan wakilai daga Afirka. Sai dai duk da CAF ta amince da goyon bayan Sheikh Salman, hakan baya nuna cewa wajibi ne dukkanin wakilan daga Afirka su zabe shi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China