Da yake karin haske game da hakan, ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Honduras Arturo Corrales, ya ce Mr. Callejas ya isa Amurka ne a ranar Litinin, bayan da a makon da ya gabata wasu bayanai suka zarge shi da hannu cikin wadanda ake zargi a waccan badakala. Mr. Corrales ya ce tsohon shugaban kasar ya isa Amurkan nen don radin kan sa, ba kuma tare da rakiyar jami'ai daga kasar ta Honduras ko Amurka ba.
Gabanin hakan dai an cafke Alfredo Hawit, wanda shi ma ya taba rike mukamin shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Honduras a kasar Switzerland, a ranar 3 ga watan nan na Disamba, bisa alakar sa da wannan bincike.
Kaza lika a wannan rana, mahukuntan Honduras sun karbi takardar sammacen mika Mr. Callejas zuwa hukumomin binciken na Amurka.(Saminu Alhassan)