Walid Muallem, ministan harkokin waje na kasar Syria dake yin ziyara a kasar Algeria ya bayyana a jiya Laraba cewa, gwamnatin kasar Syria za ta shiga shawarwarin shimfida zaman lafiya na sabon zagaye a birnin Geneva.
Walid Muallem ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labaru.
Game da batun mamaye tsohon birnin Tadmor dake tsakiyar kasar da sojojin gwamnatin kasar suka yi, Walid Muallem ya ce, wannan ba nasarar gwamnatin Syria kadai ba ce, ita ma nasarar da kasashen duniya suka samu wajen yaki da ta'addanci.
Manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya sanar a ranar 24 ga wata cewa, an kammala shawarwarin shimfida zaman lafiya na wannan zagaye a ranar 24 ga wata, kuma za a fara yin shawarwarin na sabon zagaye daga ranar 9 ga watan Afrilu.(Lami)