Jakada Fu Cong, mataimakin wakilin tawagar kasar Sin dake birnin Geneva ya yi jawabi a gun taron koli da aka yi game da batun daukar nauyin karbar 'yan gudun hijira na kasar Syria a jiya Laraba a birnin Geneva, inda ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya musamman ma kasashen da abin ya shafa su yi bincike kan dalilin barkewar rikicin kasar Syria, da kuma daukar matakan da suka dace wajen daidaita batun ta hanyar siyasa, kana da ba da taimako ga kasar Syria wajen farfado da kasar, da kuma sake mayar da 'yan gudun hijira a gidajensu, wannan shi ne hanya mafi kyau ta daidaita batun Syria.
Fu Cong ya kuma jaddada cewa, wata kasa ko wani yanki ba shi da karfin daidaita batun 'yan gudun hijira, ya kamata kasashen duniya su yi hadin gwiwa wajen tinkarar wannan batu.
Ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da kudin Sin RMB Yuan miliyan 685 ga kasashen yankin gabas ta tsakiya ciki har da kasar Syria. A halin yanzu, tana kokarin tattauna hakikanin shirin ba da taimako tare da kasashen da lamarin ya shafa da kungiyoyin kasa da kasa, domin gaggauta gudanar da wadannan ayyukan taimako.
Ban da haka kuma, Fu Cong ya ce, a nan gaba, kasar Sin tana son ci gaba da ba da taimako ga jama'ar Syria da kuma 'yan gudun hijirar kasar a kasashen waje, da kuma ci gaba da taka rawa mai yakini wajen daidaita batun Syria ta hanyar siyasa.(Lami)