Da yake gabatar da batutuwan ga sassan biyu, jakadan MDD a Syria Staffan de Mistura, ya ce tattaunawar da aka yi ta baiwa masu ruwa da tsaki damar musayar yawu, game da wasu lamurra wadanda sassan kasar suka amince da su game da makomar kasar su a nan gaba.
Wata sanarwa da tsagin 'yan adawar kasar ta Syria suka fitar, ta rawaito Mr. De Mistura na bukatar ma'aikatan ofishin sa, da su tattara bayanai na sassan da wadannan bangarori biyu suka amincewa, domin samun damar tsara zagayen taro na gaba, wanda zai maida hankali ga sauyin jagorancin kasar a siyasance.
Takardar da aka gabatarwa sassan biyu dai na kunshe da tsokaci game da amincewar su, da bukatar aiwatar da daukacin kudurorin kwamitin tsaron MDD na 2254, da na sanarwar ISSG ta taron birnin Geneva, matakin da a cewar su shi ne zai zamo jigo na warware takaddamar siyasar kasar.
Daukacin sassan biyu sun kuma jaddada daukar matakan siyasa, a matsayin hanya daya tilo ta wanzar da zaman lafiya a kasar, kana da batutuwa 12 da aka gabatar, a matsayin ginshikin kafuwar kasar Syria mai kunshe da muradun al'ummar ta.