in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Samun nasarar Syria a yaki da ta'addanci zai amfani zaman lafiyar duniya
2016-03-20 13:06:36 cri
Shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya fada jiya Asabar cewa, nasarar da kasar Syria da kawancenta zasu cimma wajen yaki da ta'addanci zata amfani duniya baki daya wajen samun kwanciyar hankali da adalci.

Kamfanin dillancin labarun kasar Syria SANA ya bayar da rahoto cewa, shugaba Bashar da tawagar wakilan kasar Iran, sun gudanar da shawarwari a wannan rana, inda suka tattauna kan sabon yanayin da kasar Syria ke ciki, ciki har da yadda ake gudanar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da yunkurin neman zaman jituwar al'umma, da kuma shawarwarin zaman lafiya da har yanzu ake yi a Geneva da dai sauransu.

A yayin shawarwarin, Bashar ya ce, goyon bayan da kasashen Iran da Rasha da dai sauransu suke baiwa Syria, ya kara azama ga jama'ar kasar wajen yaki da ta'addanci, hakan ya samar da yanayi mai kyau wajen farfado da zaman lafiya a kasar, da kuma baiwa jama'ar Syria damar samun makoma mai kyau a nan gaba.

A nasa bangare, shugaban tawagar wakilan kasar Iran Kamal Kharazi ya ce, kasarsa na tsayawa tsayin daka kan nuna goyon baya ga kasar Syria, a fannin yaki da ta'addanci da na siyasar kasa.

A jiya Asabar ne, daraktan sashen kula da harkokin daidaita rikici na kasar Rasha dake Syria, Sergei Kuralenko ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Fabrairu kasarsa ta shawarci Amurka game da hadin kai, wajen sa ido kan yadda ake gudanar da shawarwarin tsagaita bude wuta a Syria, amma har yanzu ba ta samu amsa ba. Rasha na ganin, idan Amurka ta ci gaba da hakan, to za a kara haifar da hasarar rayukan fararen hula da raunatar wasu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China