in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi bayani game da ziyarar shugaban kasar Sin
2016-04-03 13:35:22 cri

Daga ranar 28 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Czech da kuma halartar taron koli na tsaron nukiliya karo na 4 da aka yi a birnin Washington D.C. na kasar Amurka. Bayan kammala wannan ziyara, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani kan wannan rangadi.

Mista Wang Yi ya ce, shugaba Xi Jinping ya halarci bukukuwa fiye da 20 a cikin kwanaki 5 da suka gabata, ya gana da shugabannin kasashe da dama, da tuntubar mutane daga sassa daban daban, da ba da shawarar tsara manufofi, tare kuma da inganta huldar dake tsakanin kasa da kasa. Ziyararsa ta cimma burin habaka hadin gwiwa da yada tasirin Sin a duniya.

Na farko, ya daga matsayin huldar dake tsakanin Sin da Czech, da kuma inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Turai.

Na biyu, ya sa kaimi ga aikin kafa tsarin tsaron nukiliya domin daukar nauyin dake bisa wuyan kasar Sin. A game da haka, Wang Yi ya bayyana cewa, makamashin nukiliya yana samun bunkasuwa, ba a iya kyale hadarin da ake fuskanta ta fannin tsaron nukiliya ba. A cikin wannan hali, kiyaye tsaron nukiliya na duniya da rigakafin laifin ta'addanci na nukiliya na da muhimmanci sosai. Shugaba Xi Jinping ya halarci taron koli na tsaron nukiliya a wannan karo a birnin Washington D.C., lamarin da ya kasance wani muhimmin aikin diplomasiyya da kasar Sin ke gudanar a cikin sabon muhallin duniya, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai a kan wannan batu, a sa'i daya kuma, Sin tana daukar nauyin dake bisa wuyanta a fannin tabbatar da tsaron duniya bisa matsayin wata babbar kasa.

A yayin taron koli, shugabannin kasashe 6 da lamarin batun nukiliya na Iran ya shafa sun yi tattaunawa kan yadda aka gudanar da yarjejeniyar batun Iran. Xi Jinping ya ba da jawabi, inda ya bayyana matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun nukiliya na Iran, wanda ya samar da alkibla kan yadda za a gudanar da yarjejeniyar a nan gaba.

Ban da haka kuma, a yayin taron koli, Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama, ganawar da ta kasance ta farko a tsakanin shugabannin kasashen biyu a wannan shekara, wadda ta jawo hankulan kafofin watsa labaru da dama. Shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka fi jawo hankulan kasashen biyu, kana sun cimma matsaya daya a fannoni da dama.

Bugu da kari, shugaba Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe daban daban da suka halarci taron, inda suka cimma matsaya daya wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya.

Na uku, gabatar da manufofin ciki da waje da kasar Sin ke gudanar da kuma bayyana kyakkyawar makomar neman samun bunkasuwa. Wang Yi ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin ta kara jawo hankulan kasashen duniya. Kafin Xi Jinping ya kai wannan ziyara, an zartas da shirin shekaru biyar-biyar na 13 na kasar Sin a gun manyan taruka biyu na kasar, wato taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar da kuma na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, domin tsara fasalin bunkasuwar zaman al'ummar Sin nan da shekaru biyar masu zuwa.

A yayin ziyararsa, shugaba Xi ya bayyana matakan neman samun bunkasuwa da kasar Sin ke dauka, domin gabatar da kyakkyawar makomar bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, ta yadda za'a kara nuna kwarin gwiwa kan kasar Sin, da kuma kara fahimtar juna a tsakanin Sin da sauran kasashen duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China