Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Paris, babban birnin kasar Faransa a jiya Lahadi, domin halartar bikin bude taron sauyawar yanayi na Paris, bisa gayyatar da shugaban kasar Faransa Francois Hollande da kuma shugaban taron sauyawar yanayi Laurent Fabius suka yi masa.
Cikakken sunan wannan taro shi ne taron kasashen da suka kulla yarjejeniyar tsarin sauyawar yanayi ta MDD karo na 21 kuma taron kasashen da suka kulla yarjejeniyar Kyoto karo na 11, wanda za a gudanar da shi daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa ranar 11 ga watan Disamba.
Bayan bikin bude taron, shugaba Xi zai kai ziyarar aiki ga kasashen Zimbabwe da Afrika ta kudu, kana zai ba da jagora ga taron koli na dandalin tattaunawa na hadin gwiwar kasar Sin da kasashen waje a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu.(Lami)