in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Zimbabwe
2015-12-02 09:32:41 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Zimbabwe Robert Mugabe a jiya Talata a birnin Harare. Shugabannin kasashen biyu sun darajanta dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, kana sun yi hangen nesa kan makomar huldarsu tare da cimma matsaya daya kan zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

Shugaba Xi Jinping ya nanata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace kan kasashen Afrika domin kawo moriyar juna, kana za ta hada kai da kasar Zimbabwe don kara karfafa dankon zumunci a tsakaninsu domin goyon bayan juna da neman samun bunkasuwa tare. Kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Zimbabwe a fannin kare 'yancin kasar da tabbatar da tsaro da 'yancin samun bunkasuwa da kara taka rawa a harkokin kasa da kasa.

Ban da haka kuma, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afrika domin samun ci gaba ta hanyar taimakon juna. Don haka, yana sa ran cewa, zai tattauna tare da kasashen Afrika a gun taron kolin dandalin tattaunawa na hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika da za a yi a birnin Johannesburg kan shirin bunkasuwar huldar dake tsakaninsu, ta yadda za a bullo da wani kawancen inganta makomarsu.

A nasa bangare, shugaba Robert Mugabe ya nuna maraba sosai da zuwan Xi Jinping a kasar Zimbabwe. Ya ce, kasar Sin abokiyar kasar Zimbabwe ce. Kasar Zimbabwe ta jinjinawa kasar Sin saboda taimakon da ta ke baiwa kasashen Afrika, ciki har da kasar Zimbabwe.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China