A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sarkin kasar Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud sun halarci bikin kaddamar da matatar mai ta Yanbu.
Inda Xi Jinping ya bayyana cewa, hadin gwiwar da kasar Sin da kasar Saudiyya suke yi ya haifar da moriya sosai ga jama'ar kasashen biyu. Matatar mai ta Yanbu za ya biya bukatun tsarin bunkasuwar makamashi na kasar Saudiyya, kana za ta dace da shirin "hanya daya da ziri daya" na kasar Sin. Haka kuma, bangarorin biyu suna da karin ayyukan hadin gwiwa, wadanda za su kara ba da gudummawa kan hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki, da ciniki, da kuma inganta huldar abokantaka dake tsakaninsu daga dukkan fannoni.
Matatar mai ta Yanbu ita ce aikin da kasar Sin ta fi yawan zuba kudi ciki tsakanin manyan ayyukan da aka gudanar a kasar Saudiyya.(Lami)