in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya halarci liyafar taron koli na tsaron nukiliya a kasar Amurka
2016-04-01 14:00:58 cri

A jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shirya a fadar White House, ga shugabannin kasashe daban daban, wadanda ke halartar taron koli na tsaron nukiliya karo na 4.

Cikin jawabin da ya gabatar ga mahalarta liyafar, Barack Obama ya jinjinawa sakamakon da aka samu, tun bayan fara gudanar da taron koli na tsaron nukiliya a cikin shekaru 6 da suka gabata. Daga bisani kuma, ya gayyaci shugaba Xi Jinping don ya gabatar da jawabi.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa tsarin tsaron nukiliya na kasa da kasa. Da farko ya ce yanzu an soma gudanar da ayyukan ta'addanci a duniya na sabon zagaye, ciki kuwa dole ne a dora muhimmanci kan kalubalen da ta'addanci ke kawowa. Sai na biyu, a cewar sa a karkashin shugabancin taron kolin tsaron nukiliya na duniya an inganta aikin tabbatar da tsaron nukiliya a fadin duniya.

Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasashen duniya sun cimma matsaya daya kan hadin gwiwa a fannin yaki da duk wani nau'i na ayyukan ta'addanci. Kaza lika kasar Sin na fatan tattauna yadda za a karfafa tsarin tsaron nukiliya na duniya tare da bangarori daban daban, domin ci gaba da inganta wannan aiki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China