Kasar Sin za ta kira taron koli na G20 karo na 11 daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Satumba na shekarar 2016 a birnin Hangzhou na kasar Sin. A yau Talata, kasar Sin ta karbi shugabancin kungiyar G20 a hukunce, inda kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi game da taron kolin din na kungiyar.
Inda ya bayyana cewa, an fara kira taron koli na G20 daga shekarar 2008 a daidai lokacin da ake fama da rikicin hada-hadar kudi mai tsanani. A wancan lokaci, dukkan kasashe membobin kungiyar sun zama tsintsiya madaurinki daya wajen farfado da tattalin arzikin duniya, hakan ya sa aka tabbatar da matsayin kungiyar G20 na wani muhimmin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a fannin tattalin arziki a duniya.
A halin yanzu, yanayin tattalin arzikin duniya da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a fannin tattalin arziki na cikin wani muhimmin lokaci. Ya kamata mu dukufa kan raya tattalin arzikin duniya ta hanyar ingiza kirkiro sabbin kayayyaki da kuma yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki. Bugu da kari, ya kamata kasashen duniya su karfafa hadin kansu domin ingiza musayar ra'ayi a fannin tattalin arziki a tsakaninsu, da kara yin gyare-gyare kan harkokin hada-hadar kudi, da tabbatar da adalci da daidaici a fannin neman samun bunkasuwa a shiyyoyi daban daban na duniya, ta yadda jama'ar kasashe daban daban za su iya samun moriyar bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.(Lami)