in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shigar da kimanin Naira biliyan 350 cikin ayyukan bunkasa tattalin arzikin Najeriya
2016-03-23 19:53:24 cri
Ministar ma'aikatar kudi a tarayyar Najeriya Kemi Adeosun, ta ce za a samar da kudaden da yawan su ya kai naira biliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1 da miliyan dari 7, domin zaburar da tattalin arzikin kasar.

Adeosun ta bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin zantawar ta da 'yan jaridu, bayan kammala taron tattaunawa na yini biyu, na majalissar tattalin arzikin kasar.

Ta ce da zarar an rattaba hannu kan dokar kasafin kudi ta bana, za a fara sakin kudin domin raya harkokin da zasu daga matsayin tattalin arzikin Najeriya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China