in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An sake haramta shigar da shinkafa
2016-03-23 19:33:31 cri
Mahukunta a Najeriya sun sake maido da dokar nan da ta haramta shigar da shinkafa ta kan iyakokin kasar na kasa, sakamakon yawaitar ayyukan masu fasakwauri.

Cikin wata sanarwar da ya fitar game da daukar wannan mataki, kakakin hukumar hana fasakwauri ta kasar NCS, Wale Adeniyi, ya ce hukumar ta samu wagegen gibi daga harajin shigar da shinkafa cikin kasar ta hanyoyin mota. Yace hakan ne ya sa gwamnati ta ga dacewar daukar matakin dakatar da shigar da shinkafar don dakile ci gaban ayyukan sumoga wanda ya yi matukar karuwa tun daga watan Janairun da ya gabata kawo yanzu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China