in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata tura dakarunta don magance rikicin kabilanci a arewacin kasar
2016-03-20 11:42:56 cri
Rundunar sojin Najeriya zata tura jami'ai, a matsayin wani bangare na kawo karshen kashe rayukan jama'a a rikicin kabilanci tsakanin al'ummar Agatu a jihar Benue dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.

Laftanal janar Tukur Buratai, shugaban rundunar sojojin Najeriyar shine ya tabbatar da haka, a lokacin daya ziyarci sansanin sojin kasar dake kusa da Otukpo na jihar.

Babban hafsan sojin kasar, ya bayyana kwarin gwiwa na tabbatar da samun nasarar magance rikicin, ya bayyana cewar, tuni an samarwa sojojin muhimman kayayyakin da suke bukata don gudanar da aikinsu.

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankin Agatu da kewaye, yayi sanadiyyar hasarar rayukan al'umma masu yawa, tare da tilasta wasu da dama barin gidajensu.

Sai dai Buratai, ya ce, matakan da ake dauka zasu kawo karshen tashin hankalin, wanda ya addabi jama'ar yanki, kuma mutanen da suka tsere a sanadiyyar rikicin, zasu samu damar komawa gidajensu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China