Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Solomon Arase, ya ce za a aike da jami'an 'yan sanda 6,000 zuwa yankunan arewa maso gabashin kasar, domin 'yantar da al'ummar yanki daga ayyukan kungiyar Boko Haram, a wani mataki na karfafa matakan soji da ake dauka a sassan yankin.
Mr. Arase ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai a birnin Abuja fadar mulkin kasar. Ya kuma ce nan da dan lokaci rukunin farko na 'yan sandan zai isa yankunan da rikicin 'yan ta'addar ya fi shafa.
Babban sifeton 'yan sandan ya kara da cewa tura jami'an yankin zai bude sabon babi, na maida tsaro hannun 'yan sanda, yayin da dukkanin sassa da ke tallafawa harkar ta tsaro ke ci gaba da sauke nasu nauyi.
A wani ci gaban kuma, babban hafsan sojoji dake lura da matakan soji da ake dauka kan mayakan kungiyar Boko Haram manjo janar Yusha'u Abubakar, ya ce sama da garuruwa da kauyuka 80,000 ne aka kubutar, a jahohin Adamawa da Borno da Yobe daga mayakan Boko Haram, tun daga bara ya zuwa wannan shekara da muke ciki. Hakan a cewar sa ya biyo bayan namijin kokari da sassan jami'an tsaro ke yi a wadannan jahohi na kakkabe 'yan ta'adda.(Kande Gao)