An gabatar da rahoton bincike kan harkokin kula da kudi na kasar Sin a jiya Talata a nan birnin Beijing. Rahoton ya ce, yawan kudaden da Sinawa suke ajiya ta yanar gizo don neman karin riba a shekarar 2015 ya kai RMB Yuan biliyan 2000, daga cikinsu, yawan kudaden da aka ajiye ta Alipay da wasu sauran manhajoji ya kai RMB Yuan fiye da biliyan 1000.(Lami)