Za'a yi amfani da kayayyakin aiki da ya kamata domin tabbatar da cewa matsayin kudaden sun tsaya a matakin da ya dace, in ji bankin al'umma na kasar ta Sin a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Jumma'a.
Babban bankin za ta taimaki bankunan kasuwanci fadada bangaren ba da rancensu da kuma wuraren da ba su da karfin a fannin tattalin arziki ta amfani da hanyoyi da dama da suka hada da alkawarin samar da karin dama na rance da kuma matsakaicin lokaci da tsawon rancen, a cewar sanarwar.
Bankin jama'ar na kasar Sin ta ce za ta ci gaba da ingiza tsarin karban bashi don ba da dama ga bangaren kudin ya taimaki ci gaban tattalin arziki. Sannan kuma za ta ci gaba da saka matsayin kudin ruwa daidai da kasuwan da kuma inganta kafa bangaren canjin kudi da zai tabbatar da daidaito a kudin yuan, in ji sanarwar. (Fatimah Jibril)