Mai magana da yawun Bankin na duniya yace samar da sauye sauye masu ma'ana ga tsarin tabbatar da darajar kudin musaya na kasar Sin yana da muhimmanci musamman idan kasar take so inganta rawar da kasuwanni ke takawa a harkokin tattalin arzikinta .
Bankin na duniya ya kara da cewar kasar ta Sin zata iya samar da gagarumin sauyi a tsarinta na tabbatar da darajar kudin musaya cikin shekaru biyu ko uku kacal.
A ranar talatar data gabata ne Babban bankin kasar Sin ya sanar da aiwatar da wasu matakai da ya dauka, wadanda zasu tabbatar da darajar kudin musaya na kasar da dalar Amurka bisa ga sauye-sauyen harkokin hada hadar kudade a kasuwar duniya. (Ahmad)