in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mutane fiye da 600 da ake zarginsu da sa hannu cikin ayyukan ta'addanci a Pakistan
2016-03-30 11:21:06 cri
Bayan da aka kai harin kunar bakin wake a wani wurin yawon shakatawa dake birnin Lahore na jihar Punjab dake gabashin kasar Pakistan a ranar 27 ga wata, jami'an tsaron kasar sun gudanar da manyan ayyukan yaki da ta'addanci a jihar. Ya zuwa yanzu, an harbe dakaru a kalla 5 har lahira, tare da kama mutane fiye da 600 da ake zargin su da aikata laifin kai harin ta'addanci.

Kakakin bangaren soja na kasar ya bayyana cewa, an samu makamai da dama yayin da suke gudanar da wannan aikin.

Ministan shari'a na kasar Rana Sanaullah, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, bangaren soja ya gudanar da samamme a kalla sau 160 bisa ga bayanan sirri da aka samar musu.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, firaiminsitan kasar Mian Muhammad Nawaz Sharif, ya yi jawabi ta telebijin a ranar 28 ga wata, inda ya jadadda niyyar gwamnati ta kawar da barazanar ta'addanci a kasar. Kana ya ce, burin gwamnatin kasar ba wai kawar da 'yan ta'adda da kungiyoyinsu kawai ba ne, hatta ma da irin tsattsauran ra'ayi nasu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China