in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamintin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a Pakistan
2016-03-29 13:32:44 cri
Kwamintin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa a jiya Litinin, inda ya yi kakkausar suka game da harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Lahore, hedkwatar jihar Punjab da ke kasar Pakistan. Kwamitin ya bayyana cewa, zai ci gaba da nuna goyon baya ga Pakistan a yakin da kasar ke yi da ta'addanci da masu bin tsattsauran ra'ayi.

A cikin sanarwar, mambobin kwamitin sulhu na MDD sun bukaci da a bi dokokin kasa da kasa, da kudurorin kwamitin sulhu na MDD, tare da yin hadin gwiwa da hukumomin kasar Pakistan, wajen gurfanar da masu hannu cikin harin a gaban kotu.

Sanarwa ta ce, mambobin kwamitin sulhu na MDD sun yaba wa kokarin Pakistan wajen yaki da laifukan ta'addanci, tare da bayyana cewa, harin zai karfafa anniyar kwamitin sulhun wajen yaki da laifin ta'addanci. Kaza lika kwamitin ya jaddada aniyar daukar kwararan matakai, don katse kudaden 'yan ta'adda.

A ranar 27 ga wata ne aka kaddamar da harin kunar bakin wake, a wani wurin yawon shakatawa dake jihar Punjab dake yankin gabashin kasar Pakistan.

Tuni kuma kakakin gwamnatin jihar Punjab ya bayyana cewa, harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 72, tare da jikkatar wasu sama da 300. Har ila yau wani sashe na kungiyar Taliban dake kasar ta Pakistan ta dauki alhakin kaddamar da harin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China