in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mahara sun halaka mutane kimanin 25 a jami'ar Pakistan
2016-01-20 19:49:42 cri
Rahotanni daga Pakistan na cewa, a kalla mutane 25 sun mutu kana sama da 50 sun jikkata, sakamakon wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai a wata jami'a da ke gundumar Charsadda da ke arewa maso yammacin kasar Pakistan a safiyar yau Laraba.

Wani babban jami'in asibitin gundumar wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana wa manema labarai cewa, an kawo gawawwakin mutane a kalla 19 da harin ya rutsa da su.

Shi ma ministan kula da lafiyar jama'a na lardin Khyber Pakhtunkhwa, Shah Farman, ya tabbatar da jikkatar sama da mutane 50.

Kakakin sojojin Pakistan Asim Saleem Bajwa ya tabbatar a shafinsa na sada zumunta na twitter cewa, jami'an tsaro sun yi nasarar kashe a kalla 'yan bindiga 4 . Ana kuma gudanar da bincike don kamo sauran 'yan bindigan da suka gudu.

Kafofin watsa labarai sun bayyana cewa,an yi nasarar kwashe dukkan dalibai da ma'aikatan jami'ar ba tare da samun ko kwarzane ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasar Maldives Adulla Yameen ya yi allah wadai da harin ta'addancin da aka kai jami'ar ta Pakistan

Ya kuma bayyana goyon bayan gwamnati da al'ummar Maldives a kokarin da mahukuntan Pakistan ke yi na yaki da ayyukan ta'addanci.

Har yanzu dai babu wani rahoto game da ko maharan sun yi garkuwa da wasu mutane. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China