in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi bayani kan ziyarar Xi Jinping a Czech, da yadda zai halarci taron tsaron nukiliya a Amurka
2016-03-24 16:12:33 cri
A yau Alhamis ne, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya taron manema labaru, inda mataimakin ministan wajen kasar Li Baodong, da mai taimakawa Liu Haixing sun yi bayani kan ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping zai kai a kasar Czeck, da kuma yadda zai halarci taron koli game da tsaron nukiliya karo na 4 da za a shirya a birnin Washington na kasar Amurka.

Li Baodong ya bayyana cewa, shugaba Xi zai halarci taron kolin tsaron nukiliyar ne daga ranar 31 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Aflilu, inda shugaban zai yi jawabi domin bayyana manufar da kasar Sin ke bi game da batun, da sabbin matakan da kasarsa ta dauka a fannin tsaron nukiliya, gami da nasarorin da ta samu, tare da ba da shawara wajen karfafa tsaron nukiliyar duniya. A yayin taron kuma, shugaba Xi zai gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China