in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu Yandong ta kai ziyara a kasar Masar
2016-03-28 14:06:28 cri
A jiya ranar 27 ga wata, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong ta gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi da firaministan kasar Sherif Ismail.

A yayin ganawar, Liu Yandong ta bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da kulla dangantaka tsakanin Sin da Masar, kasashen biyu sun nuna goyon baya da girmamawa da kuma amincewa da juna. Yanzu ana kiyaye raya dangantakar dake tsakanin Sin da Masar. A watan Janairu na bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a kasar Masar cikin nasara, lamarin da ya nuna kyakkyawar makoma game da bunkasa dangantakar kasasshen biyu.

Ziyarar Liu Yandong a wannan karo za ta sa kaimi ga aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Shugaba el-Sisi ya bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping a farkon shekarar bana ta inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin Masar da Sin tare da hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni. Kasar Masar ta maida kasar Sin a matsayin abokiyar farko a fannin hadin gwiwar ayyukan more rayuwa da makamashi, yana fatan za a gaggauta aikin hada manufofin raya kasarsa da aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya" na Sin.

A wannan rana, Liu Yandong ta gana da babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa Nabil Elaraby a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China