A taro karo na 6 a kan tsallake kan iyaka da aka kira tsakanin kasashen biyu an fara shi ne a Khartoum babban birnin kasar Sudan karkashin jagorancin kananan sakatarori ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan da kuma ma'aikatar hadin gwiwwa da kasashen wajen na Masar.
Kwamitin har ila yau ya jaddada muhimmancin abin da aka cimma nasara ya zuwa yanzu a dalilin kaddamar da kan iyaka na Qostol-Ashkit tsakanin Masar da Sudan, in ji Abdul Ghani Al Naeem karamin sakatari a ma'aikatar harkokin wajen Sudan, a zantawar sa da manema labarai.
Shi ma a nashi bangaren Fathy Mahmoud Abdel Azim, karamin sakatare a ma'aikatar hadin gwiwwa da kasashen wajen na Masar yace a yanzu haka suna kokarin ganin yadda zasu kaddamar da kasha na biyu na tsallake kan iyakar na Arqain.
Yayi bayanin cewa sabbin shirin tsallake kan iyakan zai bunkasa ciniki da safaran kayayyakin masarufi daga Masar zuwa daukan kasashen Afrika, tare da safaran kayayyakin abinci daga Sudan zuwa kasashen Turai ta bahar rum.
Taron na yini biyu an kira shi ne domin a tantance aikin tsallake iyakar Qostol-Ashkit wanda aka kaddamar a watan Agustan bara, sannan kuma a tattauna inda shirin ya kai na kokarin kaddamar da shirin tsallake kan iyaka na Arqain.(Fatimah Jibril)