in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara kada kuri'a a zaben majalisar dokokin Masar a zagayen farko
2015-10-19 11:04:02 cri
An fara kada kuri'ar zaben majalisar dokokin kasar Masar a jiya Lahadi tun da karfe 9 na safe.

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewar, za a 'gudanar da zaben ne a wasu larduna 14 na kasar daga ranar 18 zuwa 19 ga watan nan, sa'an nan, za a gudanar da zaben a sauran larduna 13 daga ranar 22 zuwa 23 ga wannan wata, ana saran mutane miliyan 55 za su fito don kada kuri'un su a zaben.

Bayan rashin takamammiyar majalisar dokoki a kasar cikin tsawon shekaru uku, ana sa ran kasar ta Masar za ta zabi majalisar dokokin da ke da kujeru 596 kafin karshen wannan shekara, wadanda daga cikinsu, za a raba 448 ga mutanen da ba su cikin kowace jam'iyyar siyasa, sa'an nan shugaban kasar zai nada wasu 'yan majalisar 28, a yayin da jam'iyyun siyasa daban daban na kasar za su yi takarar neman sauran kujeru 120.

Rahotanni sun bayyana cewar, gwamnatin Masar ta tura kimanin sojoji dubu 180 da kuma 'yan sanda dubu 180 domin tabbatar da doka da oda a yayin zaben. Ya zuwa ranar 18 ga wannan wata, jami'an tsaron kasar, sun gano wasu boma-bomai hudu a wasu rumfunan zabe.

Zaben da aka gudanar a wannan karo ya kasance mataki na karshe da gwamnatin Abdelfattah al Sisi ta dauka bisa ga tsarin siyasar kasar. Kafin wannan, Masar ta kammala kada kuri'ar raba gardama a kan sabon tsarin mulkin kasar da kuma zaben shugaban kasar.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China