A wani rangadin gani da ido a lardin Hainan dake kudancin Sin, a ranar Alhamis zuwa Jumma'a, mista Li ya bayyana cewa yawon bude ido ya zama na dunkulewa, da ke ba da damar bunkasa sayar da kayayyakin noma da bunkasa kayayyakin masana'antu da suka dace da bukatun jama'a.
Ya yi kira ga kokarin kare muradun masu yawon bude ido, kafa wani yanayin gaskiya na kasuwa ta yadda za'a bunkasa ci gaban wannan bangare.
Ya kamata hukumomin wurin su ba da kwarin gwiwa ga harkokin masana'antu da kirkirowa, da kafa wani yanayi na hakuri game da rashin sa'a, da kafa guraben aiki sosai, a lokacin da miliyoyin daliban jami'a da suka gama karatu da daliban makarantun koyar da ayyukan hannu suke shiga kasuwar aiki a kowace shekara, a cewar mista Li.
Gwamnatocin na matakai daban daban ya kamata su daidaita hukumomi, da kyautata ayyukansu, da kuma daga wani matsayin kwarewa na hukumomi da kuma rarraba albarkatu, in ji mista Li.
Haha kuma ya yi kira ga rubanya kokari domin bunkasa sabon tattalin arziki da kirkirowa domin sabbin tsare tsaren ayyukan tattalin arziki ta yadda za'a iya kyautata ingancin rayuwar jama'a da bunkasa tattalin arziki. (Maman Ada)