A yayin ganawarsu, Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan manufarta na bude kofarta ga ketare da kuma yin gyare-gyare a cikin gida, za kuma ta tabbatar da samun bunkasuwar kasa, kyautata tsarin tattalin arziki, kara kawo wa jama'arta alheri da yin taka tsan-tsan kan abkuwar duk wata barazana.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara karfafa manufarta a fannin harkokin kudi, tare da inganta karfinta na kyautata tsarin tattalin arziki.
Bayan ganawar, Zhu Guangyao, mataimakin ministan kudin kasar Sin ya yi wa manema labarai bayani cewa, Li Keqiang da Jacob Lew dukansu sun jaddada muhimmancin huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki. A shekarar 2015, Sin ta kasance abokiyar cinikin Amurka mafi girma, kuma kasashen biyu suna kara dogaro da juna a fannin tattalin arziki da ma sauran fannoni. Huldar da ke tsakanin kasashen 2 a fannin tattalin arziki, ta kasance harsashin huldar da ke tsakanin kasashen 2, wadda kuma ta kan kara azama kan ci gaban huldarsu baki daya, don haka kasashen 2 na daukar wannan batu da muhimmanci. (Tasallah Yuan)