Shugabannin kasashe Vietnam, Laos, Cambodiyan, Thailand, da Myanmar wato kasashe 5 da kogin Mekong ya ratsa su, wadanda za su halarci taron na hadin gwiwa tsakanin kogin Mekong da na Langcang.
Kaza lika firaministan kasar Nepal Khadga Prashad Oli, da takwaransa na kasar Lithuania Algirdas Butkewiczius, da na kasar Belgium Charles Michel, da mataimakin shugaban kasar Indonesiya Jusuf Kalla, da mataimakin firaministan kasar Koriya ta Kudu kuma ministan kula da tsare-tsare da kasafin kudi na kasar Yoo II-ho, da mataimakin firaministan kasar Rasha Arkaji Dvorkovich, suma ake sa ran za su halarci taron.
A wata sabuwa kuma, bisa goron gayyatar da firaministan Sin Li Keqiang ya yi, takwaransa na kasar Nepal Oli da na kasar Belgium Michel, za su kawo ziyarar aiki nan kasar Sin a hukunce baya ga halartar taron. (Bako)