A jawabin da ya gabatar, firaministan Li ya taya Madam Lagarde murnar yin tazarce a mukamin ta. Ya ce, an kara samun rashin tabbas game da tattalin arzikin duniya, don haka ya kamata gamayyar tattalin arzikin duniya su inganta shawarwari, game da manufofi daga manyan fannoni tsakaninsu, don kiyaye zaman lafiyar tsarin hada-hadar kudi na duniya.
Har wa yau ya bayyana cewa gwamnatin Sin ta dora muhimmanci game da shawarwari na harkokin kasuwanni, da rawar da asusun IMF, da sauran hukumomin hada-hadar kudi suke takawa. Kaza lika ya yi fatan inganta shawarwari da hadin gwiwa, don kara karfafa kwarin gwiwar kasuwanni, da samar da alamar tabbatar da zaman lafiya da karuwa.
A nata bangare, Lagarde ta jinjinawa manyan tarurrukan kasar Sin biyu da aka kammala cikin nasara, ta kuma ce kasashen duniya sun dora muhimmanci sosai game da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 13, wannan zai yi amfani ga tattalin arzikin Sin wajen ci gaba da ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Kasar Sin ta kara tuntubawar kasashen waje game da darajar musayar kudin ta, matakin da ya yi matukar karfafa gwiwar kasuwannin kasashen duniya. (Bako)