Ya ce idan an kawo bangarorin Burundin waje daya aka yi tattaunawar zahiri da za'a cimma matsaya, zasu samu mafita a Burundi kuma rundunar zata ji dadin shiga cikin rundunar MAPROBU domin zata zama rundunar mai nuna hadin kai da Burundi da bada kariya ga kasar domin ganin an yi sulhu da kuma bada shawarwarin samun mafita ga Burundi. Janar Kabisa ya ce rundunar na kasashen gabashin Afrikan ya kunshi sojojin kasashe 10 da suka hada da Burundi,Comoros,Djibouti, Habasha,Kenya,Rwanda,Seychelles, Somaliya, Sudan da kuma Uganda.
A ranar 17 ga watan Disambar bara, rundunar wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU ta fitar da wani matsaya akan daukan sojoji 5,000 da aka ma lakabi da rundunar Afrika na kariya da kiyayewa a Burundin MAPROBU domin Karen kisan kare dangi da hallaka mutane ko yaushe wanda gwamnatin Burundi take yaki da shi.
A wani bangaren kuma tattaunawa tsakanin 'yan adawa dake gudun hijira karkashin shiga tsakanin Uganda ya ci tura.
Gwamnatin Burundin ta jaddada cewa ba zata shiga cikin tattaunawar da babu matsaya a zaman lafiya ba wanda take nufin wadanda suka aikata yunkurin juyin mulki a watan Mayun shekara ta 2015.(Fatimah Jibril)