in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Najeriya dake kasashen waje zasu shiga wasannin AFCON
2016-03-23 18:21:29 cri
'Yan wasan Najeriya dake kasashen ketare na daf da hallara a gida, domin shiga tawagar 'yan wasan da zasu halarci gasar wasannin share fage, na cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2017.

Za'a fafata ne tsakanin Najeriyar da kasar Masar a ranar 25 ga watan Maris a garin Kaduna, yayin da za'a buga wasa na biyu a birnin Alexandria na kasar Masar a ranar 29 a watan Maris a wasannin share fage.

Mai Magana da yawun tawagar 'yan wasan Toyin Ibitoye, ya shedawa 'yan jaridu a birnin Legas cewa, tuni dan wasan tsakiya na kungiyar Najeriyar Mikel Obi ya isa kasar da safiyar ranar Litinin data gabata, wanda hakan ya sa 'yan wasan da suka koma daga kasashen waje sun cika 4. Sauran 'yan wasan su ne Aminu Umar da Shehu Abdullahi da kuma Alex Iwobi, wadanda suka isa kasar tun a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwallon da Iwobi ya zura ga kungiyar Arsenal a wasan su da Everton a gasar Firimiya wasan ranar Asabar din data gabata, ita ta baiwa kungiyar ta sa damar lashe wasan ta da ci 2 da nema.

Ibitoye ya kara da cewa wasu 'yan wasa 6 wadanda ke taka leda a gida, na cikin jerin sunayen dake hannun kociya Najeriya Samson Siasia, cikinsu har da mai tsaron raga Ikechukwu Ezenwa, da dan wasan gaba Oghenekaro Etebo.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China