Sama da mutane dubu 40 ne suka halarci gasar, wacce aka fara a wata gadar da ta hada da Almada da kuma Lisbon.
A bangaren wasannin mata kuwa, Aga ta lashe gasar da gudun na tsawon sa'i 1 da minti 9 inda ta doke abokiyar kungiyarta Ymer Wude Ayalew da 'yar wasan kasar Kenya Linet Masai.
Yayin da a bangaren maza, Kitwara yayi nasara a gudun na tsawon mintuna 59, sai Keneth Kiprop Kipkemoi shi kuma yayi gudun sama da sa'i 1 kadan, da Paul Lonyangata wanda yayi gudun na tsawon sa' i 1 da wasu dakikoki 11.
Wasan na shekara shekara na Lisbon na rabin zango na gudun famfalaki, an fara gudanar da shi ne a shekarar 1990, kuma an kasa wannin zuwa rukunun maza dana mata, har ma da rukunun masu amfanin da kekunan guragu. Domin bunkasa harkar wasannin, masu shirya gasar su ma suka bullo da kwarya kwaryar wasan gudun famfalaki mai zongon kilomita 9.(Ahmad Fagam)