in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Van Gaal ya daidaita yanayin da yake ciki
2016-03-14 15:53:51 cri
Kulob din Manchester United dake karkashin jagorancin Mista Louis van Gaal, ya cimma nasarori sosai a 'yan kwanakin baya, inda ya lashe wasan sa da Shrewsbury Town FC da ci 3 da nema, a gasar Challenge Cup, gami da lashe wasan kungiyar da FC Midtjylland na kasar Denmark da ci 5 da1, a gasar UEFA.

Har ila yau kulaf din na Man. United ya lashe Arsenal da ci 3 da 2, gami da lashe Watford da ci 1 ba ko daya. Da wannan sakamako, kungiyar ta ci nasarar wasanni 4 ke nan a jere, wadanda kuma ta buga cikin kwanaki 10.

Sai dai nasarorin da Man. United ta samu ba abu ne mai sauki ba, bisa la'akari da yadda wasu kwararrun 'yan wasan kulob din 11, kamar su Luke Shaw, da Antonio Valencia suka kasa buga wasannin sakamakon rauni da suke da shi. Yanzu haka dai za a iya cewa kulob din ya kasance mafi fama da matsalar jin raunuka tsakanin kuloflikan dake buga gasar Premier.

Duk da haka, mista Van Gaal ya samu damar sauya yanayin da ya fuskanta a baya, inda idan ba mu manta ba, yayin da Man. United ta buga wasa da Stoke City a karshen watan Disambar da ya gabata, wasu 'yan jaridu suka yiwa Van Gaal tambaya cewar ko zai yi murabus daga matsayinsa na mai horar da 'yan wasan kungiyar ta Man. United, ganin yadda ya kasa cimma wani yanayi mai kyau ko sakamako mai ma'ana ga kungiyar, tambayar da a lokacin ta yi matukar fusata Van Gaal.

Sakamakon wasan da Stoke City ta lashe Man. United da ci 2 da nema kuwa, ya sa jaridar "The Times" ta yi hasashen cewar mai yiwuwa Van Gaal ya yi murabus cikin sa'o'i 24". Amma a karshe Van Gaal ya kare matsayinsa bisa nasarorin da kulob din na sa ya samu a baya bayan nan. A yayin da Man. United ta lashe Warford da ci 1 da nema, a gabar da takwarorinsa kamarsu Tottenham Hotspur, Arsenal, Man. City dukkansu sun sha kaye a wasannin su.

Sakamakon wasannin ya sanya mista Van Gaal yin murmushi, yana mai cewa "dukkan kungiyoyin da matsayinsu ke kusa da mu sun sha kashi." Yanzu dai Man. United ya daga zuwa matsayi na 4 daga matsayi na 6 a teburin gasar Premier, matsayin da shi da Man. City suka raba.

Nasarorin da Man. United ya samu suna da ma'ana sosai, ganin yadda kungiyar ta shiga jerin kungiyoyi mafiya karfi 8 a gasar cin kofin FA Cup, inda ta lashe Shrewsbury Town da ci 3 ba ko daya, da yadda ta shiga zagayen kungiyoyi 16 a gasar zakarun turai wato UEFA.

Duk da cewa akwai wasu manyan kuloflika da ke raina matsayin gasar zakarun turai, amma cikin wannan gasa, Man. United za ta samu damar karawa da Liverpool a zagaye mai zuwa, wanda hakan ya kara wa gasar armashi.

Yanzu haka abin da ya fi sanya Van Gaal farin ciki shi ne ganin yadda kungiyarsa ta samu damar karawa cikin kungiyoyi mafiya karfi guda 4 a tsarin gasar Premier.

A hakika, har zuwa yanzu ba za a iya cewa kulob din Man. United ya daidaita dukkan matsalolin da yake fuskantar ba. Domin har yanzu ba ya samun damar cin kwallaye da yawa, kana musayar kwallon tsakanin 'yan wasan kungiyar shi ma baya kayatarwa sosai. Bayan nazartar alkaluman nasarar kungiyar, za a iya ganin cewa kulob din Man. United na yanzu, bai sauya sosai daga yadda yake a baya ba.

Sai dai wani bangare guda da za a ce kungiyar ta samu ci gaba shi ne, yanzu ba za a ce wasannin da 'yan wasan kungiyar ke bugawa sun kasance marasa burgewa ba. Saboda 'yan wasan kungiyar a halin yanzu sun fi samun kuzari, da karfin zuciya, idan an kwatanta da yadda suke a baya.

Wasu masu nazarin wasan kwallon kafa sun yi bayani kan yadda wasan da Man. United ta buga tare da kungiyar Arsenal ya burge kowa, inda aka tashi Man. United na da nasara wato 3 da 2. An ce, a baya 'yan wasan kungiyar Man. United ba su nuna kwarewa sosai wajen kutsa kai cikin abokan karawarsu, abin da ya sanya suke kasa matsin lamba ga masu tsaron bayan abokan karawar su. Amma yanzu sun kara kokari wajen kai hari, inda suka fara yawan kai hare-hare ga kungiyoyin da suke karawa da su.

Yayin da wani mazanarci game da kwallon kafa na daban ke jinjinawa Morgan Schneiderlin, dan wasan bayan kungiyar ta Man. United, ya ce a farkon wannan kakar wasa, Morgan bai ware ba tukuna, amma yanzu ya samu daidaito da sabawa da halin da kungiyar ke ciki, inda ya sanya ido sosai kan Mesut Ozil na kungiyar Arsenal, ya kuma hana shi sakat a wasan da kungiyoyin 2 suka buga.

Idan mun duba wasannin da kulob din Man. United ya buga a baya cikin wannan kakar wasa, za mu ga yadda ya samu maki 37 kacal cikin wasannin zagaye 23 da ya halarta, matakin da ya nuna gazawar kungiyar, domin ko kungiyar da David Moyes ke horaswa ta fi haka nuna bajimta. Amma a lokacin da kusan dukkan mutane suka fara juya baya ga Van Gaal, babban kocin mai shekaru 65 a duniya ya burge masu sha'awar wasan kwallon kafa bisa manyan nasarorin da ya cimma.

Musamman ma lokacin wasan sa da kungiyar Arsenal, inda Van Gaal shi da kansa ya fadi kasa don nuna wa alkalin wasa rashin amincewa da hukuncin da aka yankewa dan wasan sa, hakan ya burge masu goyon bayan kungiyar Man. United ainun. Domin wannan kuzari, da fushi da kocin ya nuna shi ne abun da Man. United take bukata, maimakon irin zama ba tare da aikata wani abu da David Moyes kan yi ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China