in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Atletico Paranaense ya dauki hayar Paulo Autuori a matsayin kociya
2016-03-10 11:01:01 cri
Kungiyar wasan kwallon kafar Atletico Paranaense ta kasar Brazil, ta bada sanarwar daukar Paulo Autuori a matsayin sabon kociyanta, bayan da ta sallami Cristovao Borges daga wannan aiki. Autuori, mai shekaru 59 da haihuwa, ya jima ba ya aikin horas da 'yan wasa, tun barin sa kulub din Cerezo Osaka na kasar Japan.

Yanzu haka dai Autuori zai fara jagorantar al'amuran wasannin kungiyar daga ranar Asabar mai zuwa, inda shi da 'yan wasansa za su fafata da kulaf din PSTC, a wasan ajin kwararru na kulaflikan kasar Brazil.

Autuori, ya taba samun lambar yabo har guda biyu ta Copa Libertaodres a shekarun 1997 da 2005, tare da Cruzeiro da kuma Sao Paulo.

Sannan ya taba samun nasara a wasannin FIFA na cin kofin duniya a shekarar 2005, tare da Sao Paulo da kuma guda a wasannin Brazilian league championship, tare da kulub din Botafogo a shekarar 1995. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China