A cikin sakonsa, shugaba Xi ya furta cewa, ta'addanci abokin gaba ne ga dan Adam , wanda zai yi barazana ga kasa da kasa baki daya. Sin na fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin tsaro da yaki da ta'addanci, domin sa kaimi ga daidaita wannan batu yadda ya kamata, da nuna kiyayya ga ko wane irin ta'addanci, da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen biyu, har ma a duniya baki daya.
A nasa bangare, firaminista Li Keqiang ya mika sakon ta'aziyya ga takwaran aikinsa na Belgium kan wannan batu.(Fatima)